Neman Sauki Cikin Matsala (#11742)

Yā kai wanda matsala daga garēka ita cē cikakken māgani ga waɗanda suke kusa da kai, wanda takōbinka, abun ƙauna nē ga waɗanda suke son ka, wanda zūkācen māsu ƙaunarka, bā su jiran kōmi a garēka, in bā sūka ba, kuma ƙadararka ita cē abun bēgen waɗanda suka bāda gaskiya a garēka.
A cikin rangwamenka da girman ɗaukakar huskarka, ina rōƙon ka sauko mana, da abunda zā ya sā mu malmatso kusa da kai. Ka daidaita tākinmu cikin addininka, yā Allāna, ka haskaka rāyukanmu da hasken cikakken saninka, ka wāye zukātanmu da hasken sūnāyenka.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Neman Sauki Cikin Matsala (#11743)

Yabo ya tabbata a garēka, yā Allāna ! Nā nēmi shaida ga īkonka, in bā don wahala da azābar da suke daurēwa cikin bin hanyarka ba, yāyā zā a gāne da wanɗanda suke cikakkun māsu ƙaunar ka ? Yāyā zā a bambamta matsayin masōyanka da sauran ? Māsu ƙaunarka, bā su da waɗansu abukkai in bā hawāyensu ba, māsu biɗarka, bā su da waɗansu mahakurta, in bā kūkansu ba, māsu gaugautāwa zuwa garēka, bā su da wani abinci, in bā nāman zūciyarsu ba da ta ciccire.
Duk wani baƙin cikin da zai sāme ni a hanyarka, abun murna nē a garēni. Duk wasu kibban maƙiya, da zā su kafu māni don ɗaga kalmarka, abun shāwa nē a garēni. Ka bar ni, in shā cikin addininka, yā Allāna, duk abūbūwan da ka sō ni da su, kuma ka aīko mani abun da ka ƙaddaro cikin ƙaunarka.
Yā jalla ! Bā nā ƙaunar kōmi, sai abun da kake ƙauna, kuma bā ni shāwar kōmi, sai abun da kake shāwa. Nā dawwama a garēka har kullum. Ina rōƙon ka yā Allāna, ka ɗaukaka waɗanda suka bāda gaskiya ga wannan bayyanar tāka, waɗanda suka cancanta da sūnanka, kuma da mulkinka don su sāmu dāmar tunāwa da ni cikin halittarka, kuma su ɗaga garkuwar nasararka.
Kana iya aikata duk abun da kake sō. Bābu wani Allah illā kai, mai taimako cikin hallaka, mai rāya kanshi da kanshi.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Neman Sauki Cikin Matsala (#11744)

Yā Allah Ubangijina, kar ka kasance nēsa da ni, sabōda matsalōli sun māmāye ni. Yā Allah Ubangijina, kar ka bar ni in cēci kaina da kaina, alhāli ƙiyayya mai tsanani tā hayyacē ni. Ka ƙōsar da ni da tātāccen nōnon karāmarka, sabōda ƙishurwa tā kāma ni matuƙa. A ƙalƙashin fufuken rahamarka, ka kāre ni sabōda maƙiyāna sun haɗu sun zāburo mani gabāɗayansu. Tsare ni kusan gadon mulkinka, gaban alāmu māsu nūna dawwamarka har abada, sabōda ƙarfīna yā ƙāre. Da luddan ruwan murna da hannun rahamarka ya mīko, ka haƙurar da ni, sabōda baƙin ciki mai nauyi yā tsananta mani. Ka rufe ni da rīga mai zubin cikakken īkonka, sabōda talauci ya yāce ni gabāɗayāna. Ka yarda in hūta cikin saurāren tāwan kūkan kurciyar samāniyarka, sabōda baƙar darūra tā rufe ni.
A gaban gadon ɗayantakarka da hasken kyaukyawar huskarka, ka sā in tsaya, sabōda tsōro da karkarwa sun hallaka ni. A cikin kōgin rangwamenka nike sō ka zundumā ni, sabōda yawan zunubbaina sun ɓatar da ni gabāɗayāna.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Neman Sauki Cikin Matsala (#11745)

Yabo da ɗaukaka su tabbata a garēka yā Allāna. Ina rōƙon ka, don darajar shaidar māsu ƙaunarka, da hawāyen waɗanda suke tsananin buƙātar ganin ka, kar ka hana mani rahamarka a wannan babbar rānā tāka, kuma kar ka hana ni jin kūkan tantabarar nan mai wāka ɗayantakarka a gaban hasken huskarka.
Kana gani nā cikin tsananin talauci yā Ubangijina ! Gā shi nā sarkafa ga sūnanka mai mallaƙar kōmi. Nā san kat, da ina hallaka, sai gāshi nā sarkahu ga sūnanka wanda ya fi gaban hallaka. Don haka nē, nike rōƙon ka, don zātinka mai martaba, maɗaukaki, kar ka bar ni in fāɗa cikin miyāgun ayyuka. Ka riƙe hannūna cikin hannunka mai ƙarfi, ka zāgo ni daga cikin zurfin ra’ayīna karkatacce, ka hudda mani duk wani tunānīna na wōfi, kuma ka tsarkake ni da duk abun da ka yi wātsi da shi. Ka bā ni ƴancin jūyāwā gabāɗayāna wajenka, in amince da kai, in yi gudu wajenka nēman ɓūya, kuma in zābura zuwa gaban huskarka. Kai nē, hakīka, wanda kake aikata abun da kake sō don girman īkonka, kuma cikin girman īkonka, kuma haka cikin girman mulkinka kake umurtar abin da ka ga dāma. Bā wanda ya iya tsayāwa gaban ƙaddararka, bābu wanda zai iya kēwaye nufinka. Gaskiya, kai nē ƙadiran, maɗaukaki mayalwaci.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

